Dalilan Da yasa Baza mu Janye Yajin Aiki Ba – ASUU

0
168

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU tace zata cigaba da yin yajin aikin da take yi har sai gwamnatin tarayya ta biya mata bukatun ta.

A yayin da yake jawabi a jami’ar garin Port Harcourt, dake jihar Rivers, shugaban kungiyar na kasa, Biodun Ogunyemi, yace dole ne gwamanati ta fara aiwatar da rahoton ta da tayi a shekarar 2012.

Ogunyemi, wanda yayi jawabi yayin taron musayar ra’ayi na kungiyar ta ASUU tare da masu ruwa da tsaki don bayyanawa mutane irin kokarin kungiyar, yace bukatun nasu na gaske ne kuma bukatun kasa ne gabadaya.

Sannan yace dalibai sune zasu fi amfana da bukatun nasu inda ya nemi suyi duba akan hakan.

“Dalibai wadanda ya’yan mu ne kuma abokan hulda wajen cigaba yakamata su gane, abin da muke bukata daga gwammati su zai amfana kuma zai amfani kasa, gurin kwannan dalibai mai kyau, dakunan karatu daza su samar da yanayin koyarwa mai kyau, dakunan gwaji da sauran ofisoshi daza su samar da hanyar karatu mai inganci. Inji shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here