A yaune za’a fafata wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar turai

0
143

A yaune za’a fafata wasan karshe nacin kofin zakarun nahiyar turai tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Beryan munich da kungiyar kwallon kafa ta paris saint-Germany (PSG).

Za’a fara wannan gagrumin wasan ne da misalin karfe 8:00 na daren yau a filin wasa na Lisbon dake kasar Portugal.

Wannan dai shine karo na biyu da kungiyar kwallon kafa daga Germany zata hadu da takwararta daga kasar Faransa tun a shekarar 1975-76 inda kungiyar kwallon kafa ta Beryan munich ta doke kungiyar kwallon kafa ta Saint Etienne.

Kazalika wannan fafatawar za’a yitane tsakanin masu horarwa biyu kuma duk yan kasar Germany wato Thomas Tuchel da takwaransa Hansi Flick, inda kowa yake nema a karon farko.

Masu hasashe dai sunyi la’akari da irin nasarori da kungiyar kwallon kafa ta Beryan munich ta dinga samu a kwanakin baya kawo wasanta na karshe data buga inda ta lallasa kungiyar kwallon kafa ta Leon, suna ganin ita zatai nasara amman Hausawa nacewa ba’asan maci tuwoba se miya ta kare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here