Za’a dinga Yiwa Yan’ Mata Gwajin Shan Miyagun Kwayoyi Kafin ayi Aure

0
195

Mahakunta a hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA, a jiya Juma’a a birnin Maiduguri sun ce da yuwuwar shigar da yiwa yan mata gwajin shan miyagun kwayoyi kafin aure sakamakon samun yawaitar yan mata da matan aure dake ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Shugaban hukumar NDLEA, Mohammed Mustapha Abdalla, wanda yayi bayanin hakan yayin kona miyagun kwayoyi da aka kama, yace ta’ammali da miyagun kwayoyi ya kara fadada har zuwa ga yan mata da matan ma’aurata.

“Kamar yadda aka kara shirin yin gwajin shan miyagun kwayoyi zuwa ga ma’aikatan gwamnati, wannan hukuma tana duba yin hadin gwiwa da shugabannin addinai wajen yin gwajin shan kwaya kafin ayi aure a Coci-coci da Masallatai kamar yadda ake yin gwajin cutar HIV/AIDS” inji shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here