Za’a Bude Manyan Makarantu Kwanannan -Minista

0
249

Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, a yau Asabar ya tabbatarwa da daliban Najeriya cewa za’a bude manyan makarantu nan ba da jimawa ba.

Duk da bai fadi ranar daza a sake bude makarantun ba, yace zai karbi rahoto daga hukumar kula da jami’i’o ta kasa, sauran hukumomin kula da makarantu sannan ya gabatar dashi ga kwamitin kar ta kwana na fadar shugaban kasa kan yaki da annobar COVID-19.

Nwajiuba ya bayyana hakanne a yayin shirin gidan talabijin na Kasa NTA akan manufar gwamnatin Najeriya kan Ilimi da Annobar COVID-19′, Inda ya kara da cewa ya karbi kiraye-kiraye daga makarantu masu zaman kansu da jami’i’on gwamnati kan sake bude makarantun.

An dai ta yada jita-jitar cewa za’a sake bude makarantun a ranar 7 ga watan Satumba, batun da gwamnatin tarayya ta musanta.

Idan za’a iya tunawa dai an rufe makarantu ne domin dakile yaduwar cutar COVID-19.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here