Yan Sanda Sun Kara Kubutar da Yaro Dan Shekara 6 a Kano Bayan An kulle shi tsawon watanni 12 a Daki

0
234

Yan sanda a jihar Kano da masu fafutukar kare hakkin dan adam sun kubutar da wani yaro dan shekara 6 da mahaifin sa ya kulle a daki tsawon watanni 12.

Lamarin ya faru ne a unguwar Fanshekara, Hanyin Fulani, yayin da yan sanda da masu kare hakkin dan adam suka dira a unguwar tare da kubutar da yaron.

Yaron mai suna Umar Ubale, maraya ne da aka barshi riko hannun kishiyar mahaifiyar sa bayan ta rasu shekaru da suka gabata.

An kulle yaron ne a daki bisa zargin “halayya mara kyau”

Malam AA Haruna Ayagi, mai rajin kare hakkin dan adam ya taimakwa jami’an yan sanda da bayanai kan yadda ake cin zarafin yara a jihar.

Ayagi wanda yayi taron manema labarai kan lamarin yace halin da ake ciki abin damuwane matuka.

“wasu samari sun sanar damu bayan mun kammala bincike sai muka sanarwa da jami’an tsaro domin daukar matakin da yakamata”.

Ayagi yayi bayanin cewa “Daga abinda muka gano, kishiyar mahaifin sa ce silar abun da ya faru dashi na azaba”.

” Tuni muka kai yaron asibitin Murtala Mohammed domin duba lafiyarsa.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin.

DSP Abdullahi Haruna yace, mahaifin yaron, Malam Ubale yana tsare a hannun hukuma yayin da ake farautar kishiyar mahaifin yaron.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here