Masu Cin Hanci da Marasa Kishin Kasa ne Kadai Suke Sukar Buhari – Gwamna Badaru

0
144

Masu fama da matsalar cin hanci da rashawa da marasa kishin kasa sune kadai suke sukar gwamnatin shugaba Buhari.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar yayin tattaunawa da kungiyar masu amfani da kafar sadarwa na zama na jami’iyyar APC dake yankin Arewa maso yamma a Birnin Dutse.

Badaru yace”Idan aka lura da ayyukan cigaba da gwamnatin Buhari ta aiwatar a kasarnan, Buhari yayi aikin da yan Najeriya zasu yaba masa”.

Sannan yayi bayanin cewa yanayin tsaro a kasarnan ya bunkasa idan aka kwatanta da lokutan baya yayin da kungiyar Boko Haram ke kai hare-hare
“lokacin da ake kai hari ga mutane a wajen ibadar su, kasuwanni, wajen ajiye motoci da gurin taron al’umma.”

Sannan yace, “Gwamnatin Buhari ta samu nasarar kammala ayyuka masu yawa da gwamnatocin da suka shude suka fara”.

Tun farko a nasa jawabin,Shugaban matasan jam’iyyar APC masu amfani da kafar sadarwa ta zamani na yankin Arewa maso yamma, Alhaji Ahmad Rufai Gumel yace sun zo gidan gwamnatin jihar ne domin sanar da gwamnan ziyarar kungiyar a jihar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here