Kananan Yan Kasuwa Sama Da Miliyan 2 ne Suka Amfana da Tallafin Bashi na Gwamnatin tarayya -Sadiya Farouq

0
106

Gwamnatin tarayya tace kanana da matsakaitan yan kasuwa sama da miliyan 2 ne suka samu bashi wanda babu kudin ruwa aciki na shirin (GEEP) tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020.

Ministan jin kai da walwalar jama’a, Hajiya Sadiya Umar Farouq ce ta bayyana hakan yayin da take jawabi a wajen taron bikin cikar ma’aikatar shekara daya da kirkirowa a Abuja jiya Juma’a.

Shirin GEEP, wanda wani bangare ne na shirin tallafi na Kasa, yana samar da bashi karkashin tsarin TraderMoni, MarketMoni da FarmerMoni.

Sauran shirye-shiryen sun hada da shirin samawa matasa aikin yi na N-Power, ciyar da daliban makarantu da tallafin kudi ga masu rauni.

Sadiya Umar Farouq tace shirin GEEF yana bayar da Bashi daga Naira dubu 10 zuwa dubu 300 ga yan kasuwa, masu aikin hannu, masu aikin gona da sauran kananan yan kasuwa.

“Tun farkon fara shirin a shekarar 2016 zuwa yau, GEEF ya bayar da bashin da babu ruwa ga yan kasuwa miliyan 2 da dubu dari 3 domin bunkasa kasuwancin su, cewar Ministar.

Ministan ta kara da cewa, wadanda suka amfana da shirin N-power su 109, 823 daga rukunin A da B ne suka fara harkokin kasuwancin su cikin al’umma.

A batun ciyar da yan makaranta kuwa, Sadiya Farouq tace an shigar da yara sama da Miliyan 9 cikin shirin.

Sannan ministan tace gwamnatin tarayya na kan aikin samar da hukumar kula da nakasassu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here