Halin da Makusancin Buhari, Mamman Daura Yake ciki -Dansa

0
209

Daya daga cikin ya’yan Mamman Daura, Muhammad, yayi bayanin halin da mahaifin sa yake ciki, inda yace yana cikin koshin lafiya.

Rahotannin dai sun bayyyana cewa Mamman Daura wanda dan’uwa ne kuma makusanci ga shugaba Buhari, an fitar da shi zuwa kasar waje domin duba lafiyar sa a makon da ya gabata.

Sai dai Dan sa Mohammed ya shaidawa jaridar ThisDay halin da mahaifin nasa yake ciki.

Haka kuma ya tabbatar da cewa mahaifin sa bashi da matsalar wahala wajen yin numfashi.

“Mun gode Allah. Baba yana cikin koshin lafiya, bashi da matsalar rashin yin numfashi kamar yadda ake yadawa.” Inji Mohammed.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here