Ganduje Ya Aika Sakon Ta’aziyya Bisa Rasuwar Shema’u

0
297

Gwmanan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana mutuwar yar gwagwarmayar dake yaki da cutar amosanin jini a jihar Kano, Shema’u Adam Imam, a matsayin babban cikas a yaki da cutar amosanin jini a kasarnan.

“Shema’u wacce daliba ce asashin ilimin rayuwar dan adam mataki na 4 a jami’ar Bayero, kafin rasuwar ta itace shugabar masu dauke da cutar amosanin jini a Kano, wacce ta mayar da hankali wajen aikin jin kai” inji Ganduje.

“Duk da tana fama da cutar ta amosanin jini, hakan bai sa tayi kasa a gwiwa ba wajen taimakawa sauran al’umma, a fannin lafiya, ta zama tauraruwa abar misali sannan kuma Jaruma”.

“Don haka ne a madadin gwamnati da al’ummar jihar Kano, muke mika sakon ta’aziyya na rashinta ga yan’uwa da abokanta masu fama da cutar amosanin jini, yayin da muke tuna irin gibi da rashin ta ya samar.” Inji Gwamnan.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here