‘Zamu Kauracewa Taron Kungiyar Lauyoyi ta Kasa’ -Reshen Kungiyar na Jigawa

0
133

Kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Jigawa tayi barzanar kauracewa taron kungiyar lauyoyi na kasa na shekarar 2020, bayan kungiyar ta janye gayyatar da tayiwa Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna.

Jaridar PRIME TIME NEWS ta rawaito kungiyar a jiya Alhamis ta sanar da janye gayyatar da tayiwa El-Rufai na halartar taron tare da yin jawabi wanda aka tsara za’ayi shi ranar 26 zuwa 29 ga watan Agusta bayan wasu lauyoyi sun soki batun gayyatar gwamnan.

Sai dai shugaban kungiyar reshen jihar Jigawa, Garba Abubakar, a wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a yayi kira ga uwar kungiyar ta kasa ta chanza shawara, inda tace rashin yin hakan zai sa reshen kungiyar daga Jigawa kin halartar taron.

“Saboda haka muna kiran shugabanni na kasa, karkashin jagorancin shugaba Usoro San su chanza shawara nan take, ko kuma kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Jigawa taki halartar babban taron da za’ayi a yan kwanaki masu zuwa”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here