Yan’ Shi’a Sun Yabawa Kungiyar Lauyoyi ta Kasa Bisa Janye Gayyatar da Kungiyar tayiwa El-Rufai Zuwa Taronta

0
123

Kungiyar yan’uwa musulmai ta IMN ta yabawa kwamitin kungiyar lauyoyi ta kasa bisa janye gayyatar da kungiyar tayiwa Gwamna jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai a taron shekara da kungiyar zata gabatar nan gaba kadan.

Hakan na dauke ne cikin wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban sashin labarai na kungiyar, Ibrahim Musa, wadda aka rubutawa kungiyar lauyoyin a jiya Alhamis.

Kungiyar lauyoyi ta kasa dai ta janye gayyatar da tayiwa gwamnan wanda zai yi bayani a taron ne bayan lauyoyi da kungiyoyi sun yi suka tare da barazanar kin halartar taron matukar aka bawa gwamnan damar yin magana.

Wasikar kungiyar yan shi’a din ta bayyana cewa
“Kungiyar Yan’uwa Musulmi ta IMN ta lura da cewa gwamna El-Rufai bai bai dace yayi bayani ga mutanen da suka san me suke yi ba la’akari da halayyar sa ta rashin girmama doka da tauye hakkin dan adam.

” El-Rufai na goyan bayan kisan ba gaira ba dalili tare da gina babban kabari ga mamata.

“Shi, tare da hadin gwiwar jami’an soja, sun kai hari ga yan kungiyar yan’ shi’a”. Cewar Kungiyar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here