Jirgin Yakin Sojan Saman Najeriya Ya Kashe Mayakan Boko Haram da Dama a Barno

0
394

Jami’an sojan saman Najeriya na rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ sun tarwatsa sansanin mayakan Boko Haram a garin Warshale dake jihar Barno, yayin da jirgin yaki na sojan ya kashe yan kungiyar tada kayar bayan da dama.

Jami’in kula da kafafen yada labarai na ayyukan rundunar, Maj.-Gen. John Enanche, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a, ina yace rundunar na cigaba da samun sakamako mai kyau a dukkanin inda take ayyukan ta.

Mista Enanche yace an kaddamar da harin ne akan mayakan bayan samun rahotan sirri tare da yin leken asiri da dama wanda ya tabbatar da mayakan Boko Haram na amfani da wajen don shirya kai hare-hare.

Sannan yace, jirgin yaki na rundunar sojan saman Najeriya ya kaddamar da hari a wajen tare da kashe mayakan da dama.

“Rundunar Sojan Najeriya tana aiki tare da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki wajen rubanya kokarin ta na kakkabe yankin Arewa maso gabas daga yan ta’adda”.Inji shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here