An Kara Gano Wata Mata da Mijin ta Ya Kulle a Daki Har ta Mutu a Kano

0
208

Rundunar yan’sanda reshen jihar Kano ta gano gawar wata mata da mijin ta ya kulleta kwanaki uku.

Lamarin ya faru ne a unguwar Mariri dake karamar hukumar kumbotso dake birnin Kano.

An gano matar ne a kulle cikin daki bayan mijin ta ya kulle ta tsawon kwana uku.

Matar ta rasa ranta nr sakamakon kulleta da aka yi.

Sannan rahotanni sun bayyana cewa gawar matan ta fara wari ne wanda yasa makota suka fara ji har suka sanar da yan’sanda.

Mazauna unguwar sun kira yan’sanda yayin da suka kama mijin.

Mijin ya daure matar tasa ne da igiya a daki tsawon kwanaki.

Rahotanni dai sun bayyana cewa mijin ya daure matar sa da igiya a daki ba tare da bata abinci da ruwa ba tsawon kwanaki wanda hakan ya kai ga mutuwar ta.

Bayannan mazauna unguwar sun fara jin wari sai suka kira yan’sanda wanda suka samu nasarar kama mijin matar a kasuwar Mariri.

Wata majiya ta bayyana cewa yan’sanda sun tilastawa mutumin wajen bude kofar gidan domin binciken abinda ke wari a gidan, ana budewa sai aka ga matar sa daure a jikin igiya ta rasu.

Mai magana da yawun rundunar Yan’sanda ta jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da Jaridar PRIME TIME NEWS faruwar lamarin a yau Juma’a.

Sannan yace an kai gawar matar zuwa asibiti, inda ya tabbatar da cewa za’ayi karin bayani nan gaba kadan kan lamarin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here