Yan’sanda a Kano Sun Kara Kubutar da wani Mutum bayan Kulle shi Shekaru 30 a Daki

0
160

Rundunar Yan’sanda reshen jihar Kano yau Talata ta sake kubutar da wani mutum dan shekara 55 da aka kulle tsawon shekara 30 a daki bayan yan’uwan sa sun kulle shi.

Anyi zargin yana da matsalar kwakwalwa sannan shine mutum na uku da yan’sanda suka kubutar cikin mako biyu a Kano.

An samu mutumin ne a daure ajikin katako a wani daki wanda babu taga.

Sannan an sheda cewa yan’uwan mutumin mai shekaru 55 ne suka kulle shi bisa zargin yana da tabin hankali.

Mai magana da yawun rundunar yan’sanda reshen jihar Kano, Abdullahi Haruna ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Alhamis.

DSP Abdullahi Haruna yace an kwantar da mutumin a asibiti dake karamar hukumar Rogo a jihar Kano.

Sannan yace yan’sanda sun fara bincike kan lamarin.

Idan za’a iya tunawa dai cikin makwanni biyu yan’sanda sun kubutar da Ahmed Aminu, wanda mahaifin sa da kishiyar mahaifiyar sa suka tsare tsawon shekaru 7, sai wani dan shekara 30 wanda mahaifin sa ya tsare tsawon shekaru 15.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here