Wasanni: Shugaban Kasa Buhari Ya Nada Daniel Amokachi a Matsayin Mai Bashi Shawara

0
148

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana sunan Daniel Amokachi a matsayin mai bashi shawara kan
harkokin wasanni.

A wata takardar nadin nasa mai kwanan wata 17 ga Agusta kuma mai dauke da sa hannun Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, tayi bayanin cewa” Ina mai farin cikin sanar da kai cewa Shugaban Kasa Muhammadu ya amince da nada ka a matsayin mai bashi shawara kan harkokin wasanni”.

“Nadin ya fara aiki ne tun daga ranar 11 ga watan Agusta, 2020″.

A matsayin mai bada shawara ga shugaban kasa, ana zaton Amokachi zai taimakwa shugaban akan dukkan harkokin wasanni.

Amokachi wanda aka fi sani da ” Da Bull’ ya fara harkokin wasanni ne a Jihar Kaduna a kungiyar Ranchers Bess.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here