“Na Kashe shi ne Saboda yana yimin Kallon Banza”- Matashin da Ya Kashe Abokin sa akan Naira 500

0
249

Rundunar Yan’sanda reshen jihar Kano ta tabbatar da cewa wani matashi mai suna Haruna Ya’u mai shekaru 22 ana zargin ya kashe abokinsa, Ibrahim Ibrahim sakamakon fadan da suka yi akan Naira 500.

Wanda ake zargi da yin kisan, Haruna Ya’u wanda aka fi sani da Dan-Haru mazaunin karamar hukumar Tarauni ne a jihar Kano.

A wata tattaunawa da jaridar PRIME TIME NEWS tayi da kakakin rundunar yan sanda ta jihar Kano ta wayar Tarho DSP Abdullahi Haruna Kiyawa yace ana zargin Haruna ya’u ya kashe Ibrahim Ibrahin ne akan Naira 500, ya daba masa wuka a kirji, inda yayi ikirarin cewa yana yi masa kallon banza ne.

DSP Kiyawa yace “Wanda ake zargi da yin kisan ya amsa laifin da ake tuhumar sa da shi”.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, wani mutum mai suna Basiru Ahamad, wanda ya shaida abin da ya faru, ya bayyana cewa mintuna kadan kafin faruwar lamarin, matasan biyu sun fara cece-kuce a gaban sa sannan ya raba su tare da shawartar su, su zauan lafiya.

Gidan Rediyon BBC Hausa ya rawaito cewa wani abokin mamacin mai suna Sani Alhassan, yace suna tattaunawa yayin da ya dawo daga sana’ar sa ta tuka babur, sannan suka lura Ibrahim ya fadi kasa yana kiran sunan Dan-Haru.

Haka kuma, kwamishinan yan sanda na jihar Kano, Habu Sani ya tabbatar da kama wanda ake zargin, sannan ana cigaba da yin binciken kan lamarin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here