Buhari Yayi Allah Wadai da Juyin Mulkin da Sojoji suka yi a Mali

0
143

Shugaban Kasa Buhari yayi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi ranar Talata a kasar Mali, Wanda ya kawo karshen gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita.

Buhari ya bayyana damuwar sa kan abinda ya faru a kasar Mali din ne ta shafin sa na Twitter a yau Alhamis.

Inda yace Najeriya na goyan bayan matsayar da kungiyoyin kasa da kasa suka dauka na tuntuba wajen shawo kan matsalar kasar.

“Najeriya na goyon bayan kokarin Shugaban kungiyar ECOWAS Shugaba Mahamdou Issooufou, bisa tuntubar kungiyoyin ECOWAS, AU da Majalisar dinkin duniya tare da daukar matakan kawo mafita ga rikicin.

Sannan Shugaba Buhari yace samun zaman lafiya a kasar Mali kamar samun zaman lafiyar yankin yammacin Afrika ne inda yace zasu hada kai da masu ruwa da tsaki wajen dawo da kasar Mali hannun gwamnatin farar hula.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here