Shugaban Kasar Mali yayi murabus bayan sojoji sun kama shi

0
121

Shugaban Kasar Mali yace yayi murabus ne domin gudun “Zubar da jini” awanni bayan sojojin kasar sun kama shi a wani juyin mulki na bazata bayan shafe watanni ana rikicin siyasa a kasar.

Sojojin sun kulle Ibrahim Boubacar Keita da Firaminista Boubou Cisse a ranar Talata .

Dubban jama’a ne suka taru suna murna a birnin kasar.

Keita ya bayyana a gidan talabijin din kasar cikin dare inda yayi bayanin cewa bashi da wani zabe face yayi murabus nan take.

“Dole na mika mulki, saboda bana son zubar da jini” inji shi.

Babu tabbacin ko shugaban kasar yana tsare a sansanin Kati.

Kasashen Faransa da makotan kasar dai sun yi gargadin akan sauya mulki bisa tsarin da ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Shima babban Sakataren majalisar dinkin Duniya Antonio Guterres ya nami a saki shugaba Keita ba tare da bata lokaci ba inda yace kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai tattauna akan batun a taron gaggawa da zai yi a ranar Laraba.

Itama kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Africa ta yamma sun yi Allah wadai ta juyin mulkin inda suka yi barazanar rufe boda kasa da ta sama ga kasar ta Mali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here