Sarkin Karaye Ya nada Sabon dagacin garin Kafin Agur

0
209

Sarkin Karaye, Alhaji Dr. Abubakar Ibrahim II a yau ya nada Ahamd Iliyasu a matsayin dagacin garin Kafin Agur dake karamar hukumar Madabi.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in yada labarai na masarautar Karaye, Haruna Gunduwawa ya fita tace nadin yazo ne bayan karbar rahoto daga hakimin Madobi, Alhaji Musa Sale Kwankwaso kan yadda masu zabar dagaci na garin Kafin Agur suka gudanar da zabe wanda Ahamd Iliyasu ya samu nasara.

Sanarwar ta kara da cewa Sarkin Karaye, ya bukaci Dagacin ya zauna da mutanen sa lafiya da gaskiya.

Malam Ahamad ya gaji mahaifin sa ne wanda ya rasu kwanan nan.

Haka kuma sarkin ya karbi mutanen garin Agalawa dake karamar hukumar Madobi da Manajan kamfanin Bua a fadar Ndoji.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here