Mutane Dubu 25 ne Suka Mutu Sakamakon Cutar COVID-19 a Yankin Afrika-WHO

0
113

Ofishin Hukumar lafiya ta duniya(WHO) na yankin Africa dake Brazzaville na Kasar Congo yace an samu asarar rayuka 25, 000 sakamon cutar COVID-19 a Africa.

Hukumar lafiyar ta bayyana hakanne a shafin ta na Twitter @WHOAFRO.

WHO ce tayi bayanin cewa”Akwai sama da mutane Miliyan Daya da suka kamu da cutar COVID-19 a Yankin Afrika, Mutane 846, 000 ne suka warke yayin da mutane dubu 25 suka rasu.

Kasar South Africa tana da mutane 589, 886 wadanda suka kamu da cutar da mutane 11, 982 da sukaa mutu, sai Najeriya dake biye da ita da mutane 49, 485 da aka tabbatar sun kamu da cutar yayin da mutane 977 suka rasu, sannan kasar Ghana mai mutane 42, 653 da suka kamu sannan mutane 239 suka mutu.

Sannan tayi bayanin cewa Kasar Seychelles, Eritrea da Mauritius sune kasashen da basu da masu dauke da cutar dayawa.

Ofishin yace Kasar Seychelles tana da mutane 127 da suka kamu da cutar sannan ba wanda ya rasu sakamakon cutar, sai Eritrea mai mutane 285, sannan kasar Mauritius mai mutane 346 da mutane 10 da suka rasu.

A wata sanarwa da ta sanya a shafin ta WHO tace a ranar 14 ga watan Agusta ne yayi daidai da wata 6 da samun bullar cutar a Afrika.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here