Mali: ECOWAS ta umarci Sojojin kasashen Yammacin Afrika su kasance cikin shirin Ko ta Kwana

0
146

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma(ECOWAS) ta dakatar da kasar Mali bayan sojoji sun yi juyin mulki a kasar, sannan kungiyar ta umarci sojojin kasashen yammacin Afrika su zauna cikin shirin ko ta kwana.

Sojoji dai a kasar Mali sun kwace mulki daga hannun shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita da Firaministan Kasar, Boubou Cisse, inda suk tilisata masa yin murabus bayan shafe watanni al’ummar kasar na zanga-zangar kin jin gwamnatin sa.

Kungiyar ECOWAS tace biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, kasar Mali an dakatar da ita har sai an dawo da shugaban da kundin tsarin mulki ya tanadar.

Sannan kungiyar ta nemi a gaggauta aiwatar da takunkumin da aka sawa sojojin da masu taimaka musu.

“ECOWAS ta nemi a samar da jami’an tsaron ko ta kwana na kungiyar”

“Sannan kunigar ta yanke shawarar rufe iyakar kasar ta Mali tare da dakatar harkokin kasuwanci, da kudade”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here