‘Kishiyar Mahaifiya ta ce Silar Kulle ni Shekara 7 a Gareji’ -Ahmad Aminu

0
205

Tattaunawa kenan da wakilin jaridar PRIME TIME NEWS yayi da Ahmad Aminu, mai shekaru 32 wanda mahaifin sa da kishiyar mahaifiyar sa suka kulle tsawon shekaru 7 a garaejin mota na gidansa dake unguwar Farawa, ta Karamar hukumar Kumbotsa a jihar Kano.

Wakilin Jaridar PRIME TIME NEWS ya tattauna da mutumin ne a Asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake Kano.

Ga Yadda Tattaunawar ta Kasance:

Da Farko dai zamu so muji cikakken sunan ka.

Sunana Ahmad Aminu.
Abin da zan iya cewa shine kawai na ziyarci gidan mahaifina ne yayin da wannan abin ya faru dani. An kulle tsawon shekara 7 ba tare da dalili ba. Abin da ya faru tsakani na kannena maganar gaskiya nasan ban yi wani laifi ba.

Me ya faru tsakanin ka da kannen ka wanda aka ce shi taimaka ka tsinci kan ka a wannan hali?

Abin da ya faru shine ina tare dasu ne a wani waje sannan basa jin dadin wasu abubuwa da nake yi, hakane yasa su kishi. Na ziyarci gidan mahaifina

Kasan inda kake a yanzu?.

Eh, nasani ina asibiti yanzu amma Asibitin zana ne ko na Asibitin kashi.

Zaka iya fada mana adadin kwanakin da kayi anan Asibiti?

Eh, zan iya cewa nayi kwanaki biyu, amma abokaina suna tambaya ta shin nasan abin da ke faruwa. Nura Zangina da Babani suna tambaya ta abin da ya faru, na fada musu cewa bansan komai ba. Suna so ne kawai su bata min suna a unguwar mu.

Ya alaqa take tsakanin ka da mahaifin ka??

Alaqata da mahaifina alaqa ce mai kyau, amma akwai sabani tsakanina da kishiyar mahaifina. Akwai lokacin da Babana ya taba gayamin cewa na dauki kishiyar mahaifiyata a matsayin uwa sai dai ni na dauke ta ne a matsayin yayata. Wannan shine babban dalilin shiga matsala ta.

Yaya kake ji yanzu?

Yanzu ina jin sauki, duk da bani da karfin jiki, sannan bani da isasshen jini a jikina sannan ina shan wuya. Yayin da aka kawoni nan an bani Burodi, shayi da kosai.

Shin Kayi Karatu na Islamiyya ko na Boko?

Eh, naje karamar makarantar Firamare. Da makarantar gaba da firamare. Nayi Islamiyya bazan iya tuna sunan makarantar da nayi ba. Ina da mata da yara.

A lokacin da kake a kulle me kake yi a kullum ?

Yayin da nake a kulle ana bari na nayi Alwala nayi Sallah, naci abinci, nayi bacci.

Me kake tunanin yasa aka kulle ka tsawon shekara 7?

Dalilin shine suna yimin hassada akan abinda nake dashi a lokacin. Sabida nafi su.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here