Gwamnatin Jihar Kano ta Ayyana Gobe Alhamis a Matsayin ranar hutu

0
212

Gwamnatin jihar Kano ta ayyana gobe Alhamis, 20 ga watan Agusta a matsayin ranar hutu domin murnar bikin sabuwar shekarar musulunci ta 1442.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba wacce aka fitar yau a Kano tace Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci mabiya addinin musulunci a jihar suyi da suyi amfanin da lokacin bukukuwan sabuwar shekarar wajen yin addu’ar samun zaman lafiya da cigaban jihar.

Ganduje yayi addu’ar neman daukin Allah kan matsin tattalin arziki da ake fuskanta wanda annobar covid-19 ta haifar. Sannan yayi kira ga jama’a suji tsoron Allah a dukkan al’muran su kuma su zauna lafiya tsakanin su.

Daga karshe Ganduje ya tabbatar da cewa gwamnatin sa zata cigaba da samar wal-wala da ayyukan cigaban jihar Kano.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here