Silar Jaruma Hafsat Idris(Barauniya) Na Fara Waka -Mawaki Ameer Dan Soja

0
639

 

Shahararren mawakin Hausar nan wanda aka fi sani da Ameer Dan Soja ya bayyana cewa silar kaunar da yake yiwa jaruma a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Hafsat Idris wacce ake kira da ‘Barauniya’ ce tasa ya fara waka.

Mawakin wanda dan asalin unguwa uku ne dake karamar hukumar Tarauni a jihar Kano ya bayyana hakanne yayin tattaunawa da jaridar PRIME TIME NEWS yau a Kano.

An tambayi mawakin kan yadda ya tsinci kansa a fannin waka, inda yace ya fara waka ne saboda yadda jaruma Hafsat Idris ke burge shi.

“Na tsinci kai na ne a fannin waka ta bangaren silar wata jarumar Hausa Film, saboda tana burge ni, fina-finan ta suna burge ni, saboda burge nin da take nace bari nayi mata waka, shine na tsaya nayi mata waka ta yabo daga nan na cigaba da yin waka”. Cewar Mawakin.

Ameer Wanda ake yiwa laqabi da Ameer Dan Soja yace ya samo laqabin ne daga wani maigidan sa da ake kira ‘Sagir Dan Soja’.

Mawakin ya shaidawa jaridar PRIME TIME NEWS cewa yayi wakokin kusan guda 50 wadanda aka sake su, sannan yace cikin wakokin nasa yafi kaunar wakar ” AKAN KI NE” Wacce ba’a jima da Sakin ta ba.

Sannan mawakin yace ya fuskanci qalubale a sanda ya fara waka tun daga gida da kuma matsalar kayan aiki, haka kuma ya bayyana yadda al’umma suke sauraron wakar sa a matsayin babbar nasara.

Daga karshe mawaki Ameer Dan Soja yayi godiya da fatan Alkhairi ga masoyan sa masu sauraron wakokin sa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here