Sama da Yan Najeriya Dubu 20 ne Suka Samu aikin yi Sakamakon aikin gina layin dogo -Minista

0
135

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi yace sama da yan Najeriya dubu 20 ne aka dauka aikin gina layin dogo daga jihar Legas zuwa Ibadan.

Amaechi ya fadi hakanne a wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin inda yace an dauki ma’aikatan ne kamar yadda tsarin dokar yarjejeniyar da Najeriya ta kulla da Kasar China na gina layin dogon da zai ci kudi Biliyan 1.6.

Ministan yayi bayanin hakan a yayin zaman jin ra’ayin jama’a da kwamitin majalisar wakilai keyi.

“Akwai yan Najeriya dubu 20 da aka dauka aiki a cigaba da gina layin dogo daga jihar Legas zuwa Ibadan, yan kasar 560 ne kadai ke aiki a wajen gina layin dogon” cewar Ministan.

“Yawancin kayayyakin aikin da ake amfani dasu an samar da su ne a Najeriya, banda wadanda ake kera su a kasashen ketare.”

“Muna da Yan Najeriya sama da 150 da muka horar da su a matsayin Injiniyoyi a Kasar China. Sannan kasar China ta gina makarantar horarwa guda biyu a kasarnan, daya a Idu da jami’ar Sufuri a Daura jihar Katsina.”

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here