Majalisar Koli ta Addinin Musulunci ta bukaci Ganduje Ya zartar da Hukuncin Kisa kan Wanda yayi batanci ga FIYAYYEN HALITTA S.A.W

0
135

Majalisar koli ta addinin musulunci ta Najeriya, ta bukaci gwamnatin jihar Kano ta zartar da hukuncin da kotu ta yanke kan mawakin da yayi batanci ga ANNABI MUHAMMAD S.A.W a Kano.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban magatakardar majalisar, Nafi’u Baba-Ahmad, a yau Talata a Kaduna, majalisar shari’ah din tace zartar da hukuncin zai zama izina ga wasu.

Sannan taga baikon masu yin kira a yafewa wanda ya aikata laifin, sannan ta bawa gwamnatin jihar Kano shawara kar ta saurare su.

“Kiran da wasu masu ikirarin kare hakkin dan’ adam suke yi na cewa a yafewa wannan mai laifin bazai yi tasiri ba wajen hana gwamnatin Kano aiwatar da abinda yake shine dai-dai.

” Lamarin abinda ya shafi addinin musulunci ne kadai, kuma ba mutanen Kano kadai ba, mafiya yawan yan Najeriya wadanda musulmai ne”.

“Majalisar Koli tana son shedawa yan Najeriya musamman kungiyoyin kare hakkin dan adam cewa hukuncin yana kan tsarin kotun koli ta Najeriya.

” Sannan muna yin kira ga dukkan muslmai su kiayye harshen su kamar yadda ANNABI MUHAMMAD S.A.W ya fada “Duk wanda ya yarda da Allah da ranar Lahira ya fadi Alkhairi ko yayi shiru”.

Idan za’a iya tunawa dai, wata kotun shari’a a Kano a ranar 10 ga watan Agusta ta yanke hukuncin kisa kan Yahaya Sharifai bayan samun sa da laifin yin batanci ga FIYAYYEN HALITTA S.A.W.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here