Kamar Yadda Aka Hada Bidiyon Ganduje na Dala Haka aka Hada Nawa na Fito da Bindiga -Bakwana

0
203

Ofishin mataimakin Sufeton Yan sanda shiyyar Kano ya gayyaci mai taimakawa gwamnan jihar Kano kan sha’anin siyasa, Mustapha Buhari Bakwana, don amsa tambayoyi bisa zargin fito da bindiga tare da umartar magoya bayan sa su kashe wadanda suke adawa dashi.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, a wani Bidiyo da ya dinga yawo a kafafen sadarwa na zamani, an ga Bakwana ya fito da Bindiga tare da yan Daba wadanda aka tabbatar da magoya bayan sa ne yayin taron sulhu na jami’iyyar APC.

Kwamitin, wanda tsohon kakin majalisar dokokin jihar Kano, Kabiru Rurum ke shugabanta ya zauna ne a karamar hukumar Kumbotso domin yin sulhu.

Sai dai an kai karar Bakwana ne bayan an samu arangama tsakanin magoya bayan sa a wajen sulhun.

Haka kuma, a wata tattaunawa da gidan Rdiyon Freedom a Kano, Bakwana ya musanta batun Bdiyon inda yace makiya ne suka hada Bdiyon Kamar yadda aka hada Bidiyon Ganduje na karbar Dala.

Mai magana da yawun shiyyar Yan sanda ta Zone 1, Rabilu Ringim, ya tabbatar da cewa Bakwana yana tsare a hannun su domin amsa tambayoyi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here