Buhari na kan aikin tsamo yan Najeriya Miliyan 100 daga talauci -Gwamnatin tarayya

0
149

Gwamnatin tarayya ta jaddada aniyar shugaban kasa Muhammadu Buhari na tsamo yan Najeriya Miliyan 100 daga talauci cikin shekaru 10.

Sannan tace gwamnatin shugaba Buhari zata bar kuduri mai kyau na gaskiya wajen kashe kudin al’umma, yin komai a bude ba tare da yin rufa-rufa ba ta hanyar shirin ta na Open Government Partnership(OGP).

Karamin ministan kasafi da tsare-tsare, Prince Clem Ikanade Agba, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja awajen ginin bayar da horo ga masu taimakawa ministoci.

“A iya sanina, wannan ne karo na farko a tarihin kasarnan da aka hada dukkan masu taimakawa ministoci wajen daya domin basu horo.

Itama anata jawabin, Babban sakatare a ma’aikatar kasafi da tsare-tsare ta kasa, Mrs Olushola Idowu cewa tayi shirin na musamman ne kamar yadda aka tsara shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here