Hukumar DSS ta Saki Ghali Umar Na’abba

0
189
Ghali Umar Na'abba

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS sun saki Ghali Umar Na’abba, tsohon kakakin majalisar wakilai ta kasa kuma shugaban kungiyar National Consultive Forum.

Na’abba, wanda ya shafe tsawon awannin biyar yana amsa tambayoyin hukumar an sallame shi mintina kadan da suka wuce, sannan yana kan hanyar sa ta zuwa sakatariyar kungiyar NCF dake Utako, Abuja don yin bayani ga mambobin kungiyar da yan Jarida.

Jami’an tsaron farin kayan sun gayyaci Ghali Na’abba ne kwanaki hudu da suka wuce bayan ya gabatar da wani shiri a gidan Talabijin.

A cikin shirin, Ghali Na’abba ya soki gwamnatin shugaba Buhari ta bangaren gazawa wajen samar da tsaro, matsin tattalin arziki.

A

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here