Hotunan da Mawaki Ado Gwanja Ya wallafa a shafin sa sun jawo ce-ce-kuce

0
352

Shahararen mawakin Hausa kuma jarumi a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood Ado Gwanja ya wallafa wasu hotuna a shafin sa na Instagram inda suka jawo ce-ce-kuce.

Mawakin ya wallafa hoto na farko ne wanda aka ganshi tare da wasu yan mata inda ya rubuta cewa “Duk wani mai abun fada ga dama”.

A inda mabiya shafin nasa suka dinga bayyana ra’ayoyi ma ban-ban ta.

Wani mabiyin shafin mai suna
Official Zaharaddeen ya bayyana ra’ayin sa da cewa “adai ji tsoron Allah”.

Sai wani mai suna Bundialigas yace ” tom naji amma matan basu yimaka yawa ba”.
Real Saadatu yau ahmed tace “can ta matse ma rayuwar ka ce ba ta wani idan kayi mai kyau kan ka”.

Hakanan Ado Gwanja ya kara wallafa wani hoton inda yake a tsaye wata budurwa na tsugune a gefan sa inda ya rubuta ” Kwatance baya yiwa mage ragama sai da 👀 da 👁.

Inda kusan mutane 500 suka bayyana ra’ayoyin su ma ban-banta yayin da wasu suke suka ga hotunan wasu kuma suke yabon sa.

Ado Gwanja dai, shararren mawaki ne da yayi fice a kwanakin baya, ko dayake wasu na ganin har yanzu tauraruwar sa na haskawa yayin da wasu ke ganin mawaka irin su Hamisu Breaker sun sha gaban sa a halin yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here