COVID-19: Za’a Dawo da Zirga-Zirgar Jiragen Kasashen Ketare

0
178

Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar 29 ga watan Agusta a matsayin ranar da za’a dawo da zirga-zirgar jiragen sama na kasashen ketare.

Hadi Sirika, Ministan zirga-zirgar jiragen sama ne ya sanar da hakan a yau Litinin inda yace kamar yadda aka fara zirga-zirgar jiragen cikin gida da filayen tashi da saukar jirage na Legas da Abuja haka ma dasu za’a fara ta kasashen ketare.

“Ina mai farin cikin sanar da dawowa da zirga-zirgar jiragen kasashen ketare daga 29 ga watan Agusta. Inda za’a fara da filayen tashin sauka da jirage na Lagos da Abuja.”

“Zamu sanar da ka’idojin da za’a bi a lokacin da yadace. Muna godiya bisa hakurin ki.” Inji minsitan a sakon da ya wallafa a shafin Twitter.

Najeriya dai ta rufe filayen jirgin sama ne a ranar 23 ga watan Maris, domin dakile yaduwar cutar Corona.

Jigila jirage ta cikin gida ta fara ne a ranar 8 ga watan Yuli da filayen tashi da saukar jirage na Lagos da Abuja yayin da filayen sauka da tashin jirage na Kano, Port Harcourt, Owerri da Maiduguri suka bude a ranar 11 ga watan Yuli.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here