Yan’sanda Sun Kubutar da Dan Shekara 35 Bayan Mahaifin Sa Ya Kulle Shi Shekaru 15 a Daki

0
164

Rundunar Yan’sanda reshen jihar Kano a yau Lahadi ta sake kubutar da wani mutum wanda ake zargin mahaifin sa ya kulle shi tsawon shekaru 15, kwana uku bayan an kubutar da wani mutum bayan mahaifin sa da kishiyar mahaifiyar sa sun kulle shi shekaru 7.

Mutumin da aka kubutar din dai mai suna Ibrahim Lawan, dan shekara 35 an kulle shi a daki tsawon shekara 15.

Mahaifin nasa mai suna Mallam Lawan, Limamin Masallacin Juma’a ne.

Lamarin ya faru ne a unguwar sheka tsawon shekaru ba’a bar mutumin yaga koda hasken rana ba.

Tawagar jami’an yan’sanda bangaren kiwon lafiya da jami’an Puff Adder.

Mai magana da yawun rundunar yan’sanda reshen jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da jaridar PRIME TIME NEWS faruwar lamarin yau a Kano.

DSP Abdullahi Haruna, yace mutumin da aka kubutar mai suna Ibrahim Lawan an mika shi zuwa asibiti sannan an fara gudanar da bincike kan lamarin.

Idan za’a iya tunawa dai rundunar yan sanda ta Kano ta kubutar da Ahamd Aliyu mai shekaru 32 wanda mahaifin sa da kishiyar maihaifiyar sa suka kulle shekaru 7 a daki.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here