Yadda Bidiyon Dala Ke Kawo Cikas Ga Ganduje

0
784

An caccaki gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a kafafan Sadarwa na zamani bisa ikirarin da yayi na cewa gwamnatin sa baza ta saurarawa masu karbar cin hanci da rashawa ba a jihar.

Kamfanin dillacin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa, Ganduje ya fadawa shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhyi Magaji cewa kar a kyale duk wanda aka kama da cin hanci da rashawa.

Gwamnan yayi alkawarin cewa bazai yi katsalanda ba akan zargin cin hanci da rashawa da ake yiwa mutane a jihar.

Sai dai a shekarar 2018 ne gidan Jaridar Daily Nigerian ya wallafa wani faifan bidiyo dake nuna gwamnan na karbar Daloli daga hannun dan kwangila.

Faifan Bidiyon ya jawo cece-ku-ce a kafafan Sadarwa, wanda shugaban kasa Buhari ya bayyana shakkun sa kan fasahar da aka yi amfani da ita wajen daukar bidiyon.

Sai dai Majalisar dokokin jihar Kano ta fara bincike kan lamarin kafin wata kotu a Kano ta dakatar da binciken.

Duk da wannan zarge-zarge, Ganduje ya samu damar lashe zabe a karo na biyu tare da more dokar kariya daga tuhuma.

Sai dai wasu yan Najeriya sun nuna rashin jin dadin su kan yadda Ganduje yake ikirarin yaki da cin hanci da rashawa.

A Shafukan Sadarwa na Twitter da Facebook yan Najeriya da dama sun bayyana ra’yin su kan ikirarin Gwamnan na yaki da cin hanci da rashawa.

Duk da cewa gwamnatin jihar ta Kano tasha musunta batun faifan bidiyon, yan adawa na amfani dashi wajen sukar gwamna Ganduje a duk lokacin da yayi wata magana ta yaki da cin hanci da rashawa.

Ko a kwanakin baya ma sai da gwamnan jihar Rivers Wike yayi gugar zana ga Gwamna Ganduje kan bidiyon Dollar bayan Ganduje yace “zasu killace Wike” yayin zaben gwamnan jihar Edo.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here