Rashin Tsaro: Buhari Ya Watsa Mana Kasa A Ido – Dattijon Arewa

0
168

Wani mai rike da sarautar gargajiya a jihar Barno, Zanna, yace duk da ikirarin da ake yi, shugaba Buhari ya gaza wajen kawo karshen matsalar tsaro musamman a yankin Arewa maso Gabas.

Alhaji Hassan wanda shine Zanna Boguna na jihar Barno ya fadi hakanne yayin tattaunawa da kafar sadarwa ta Arewa Agenda.

Inda yace, yawaitar hararen da kungiyar Boko Haram take kaiwa, yin garkuwa da mutane a manyan hanyoyi na daga cikin barazanar rashin tsaro da ake fuskanta.

Boguma wanda mamba ne a kungiyar dattawa ta Arewa, ya soki gwamnatin tarayya bisa kin yin abubuwan cigaba a yankin Arewacin kasarnan duk kuwa da irin gudunmawar da suka bayar wajen kafa gwamnatin.

“Idan ana batu na Najeriya Buhari kawai ya dora yan Arewa akan mukamai ne amma basu yi wani abun azo a gani ba na cigaba. Yan ta’adda na kashe yan Arewa ba tare da kawo karshen lamarin ba. Janar Buhari, eh! Mu muka zabe shi, da yawan kuri’un arewa ya zama shugaban kasa”. Inji shi.

Boguma yace kungiyar dattawan Arewa tayi aiki tukuru wajen ganin Buhari ya zama shugaban kasa, ciki har da nunawa kasar Amurka bukatar ta goyi bayan takarar sa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here