Jami’ar Bayero Tayi Gwajin Samfur 27, 831 na Cutar Corona

0
171

Mataimakin shugaban jami’ar Bayero Kano mai barin gado Farfesa Yahuza Bello Yace cibiyoyin gwajin cutar COVID-19 guda uku da jami’ar ta samar sun yi gwaji 27, 831.

Yahuza Bello ya fadi hakanne a yau Lahadi yayin bude sabon dakin taro na kasa da kasa a kwalejin koyar da ilimin lafiya ta jami’ar dake asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.

Inda ya kara da cewa cikin samfur 27, 831 da ayiwa gwaji, dubu 13 sun fito ne daga Kano yayin da ragowar suka fito daga jihohin Jigawa, Yobe, Kaduna da Jihar Katsina.

Hakanan ya kara da cewa, jami’ar ta kashe kudi Miliyan 80 wajen samar da kayan aiki ga cibiyoyin gwajin guda uku, sannan har yanzu jami’ar na samo kudade domin cigaba da samar da kayan aiki ga cibiyoyin.

Mista Bello yace Cibiyoyin suna daga cikin cibiyoyi hudu da suka yi fice a kasarnan kamar yadda hukumar NCDC ta bayyana.

“NCDC ta ayyana cibiyoyin gwajin BUK a matsayin wadanda suka yi fice a Najeriya.

” Hakan ya faru ne sakamakon jami’a ta kashe miliyoyin kudi domin inganta su.

“Daga Kudin shigar da BUK take samu, mun bayar da Naira Miliyan 50 domin siyan kayayyakin aikin.”

Yayin da yake jawabi, Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa jami’ar bisa kokarin ta na kafa cibiyoyin.

Inda yace cibiyoyin sun taimaka matuka wajen rage samun masu kamuwa da cutar a jihar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here