
Daga Muhammad Bashir
Gwamnatin jihar Kaduna tace yan ajin karshe na kananan makarantun Sakandire zasu koma karatu a ranar Lahadi 16 ga watan Agusta da Ranar Litinin 17 ga watan Agusta.
Mr. Phoebe Sukai-Yayi, babban sakatare a ma’aikatar ilimi ta jihar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka aikowa jaridar PRIME TIME NEWS.
Sukai-Yayi yace ma’aikatar ta yanke shawarar hakanne domin domin bada damar yin shirye-shiryen zana jarrabawar(BECE) wacce za’a yi a ranar 24 ga watan Agusta.
Jaridar PRIME TIME NEWS ta samu bayanin cewa, an umarci dukkan shugabannin makarantun Sakandire a jihar da suyi shirin da yakamata na karbar daliban makarantun kwana a ranar Lahadi, 16 ga wata da na makarantun jeka ka dawo a ranar Litinin 17 ga watan na Agusta.