Kar Ka Saurarawa Duk Wanda aka kama da Cin Hanci Da Rashawa Ganduje Ga Muhyi Magaji

0
164

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya fadawa shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar korafe-korafe ta jihar Kano, Muhyi Magaji Rimin Gado, kar ya nuna ban-banci a yaki da cin hanci da rashawa a jihar.

Haka kuma gwamnan ya fadawa Muhyi cewa yanzu ba lokacin da za’a kyale wanda aka samu da cin hanci da rashawa ba ko da kuwa yana daga cikin mukarraban gwamnati.

Gwamnan ya fadi hakanne yayin ziyarar duba aikin gyara shelkwatar hukumar a jihar.

Ganduje yace, gwamnatin tarayya ita kadai baza ta iya yaki da cin hanci da rashawa ba sai jihohi da kananan hukumomi sun yi koyi.

“Duk wanda ya fada komar hukumar yaki da cin hanci da rashawa zai fuskanci sakamako. Ba ruwana a ciki, bazan taba yin katsalanda ba akan kowanne lamari na hukumar.
Don haka kar a aji tsoron kowa ko da kuwa acikin mukarrabai na ne”. cewar Ganduje.

Yayin da yake jawabin maraba tunda farko, Muyhi Magaji Rimin Gado ya yabawa Ganduje kan yadda yake yaki da cin hanci da rashawa a jihar, inda yace “kokarin ka na siyasa da goyan bayan ka ne yasa wannan hukumar tayi fice a fadin kasar nan.”

Idan za’a iya tunawa dai hukumar akwana-kwanan ne dai ta mayar da kudaden malamai wanda aka yi zargin mai taimakawa gwamna kan sha’anin yada labarai ya rage musu bayan sun yi addu’a a gidan gwamnatin jihar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here