Ganduje Ya Bada Umarnin Kara Yawan Kudin Tallafin Karatu Ga Dalibai Yan Asalin Jihar Kano

0
290

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje yace ya bada umarnin sake duba kudin tallafi da gwamnatin jihar take bawa daliban manyan makarantun gaba da sakandire don kara yawan sa duba da halin da ake ciki na matsin tattalatin arziki.

Ganduje ya fadi hakanne a yau yayin bude bikin makon matasa, acigaba da bukukuwan ranar matasa ta duniya.

Taron wanda ya samu halartar manyan jami’an gwamnatin jihar Kano, kungiyoyin matasa, matasa masu yiwa kasa hidima da kungiyoyin kwallon kafa, an gabatar da shi a rufaffen dakin taro na filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a Kano.

Ganduje yace “Duba da irin halin da ake ciki na matsin tattalin Arziki na bada umarnin sake duba alawus-alawus da ake bawa dalibai don a kara yawan sa”.

Sannan, Ganduje ya kara da cewa gwamnatin sa ta samawa matasa da dama aiki ciki har da daukar nauyin matasa 600 wajen koya musu gyaran mota na zamani.

Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin sa ta shigar da matasa da dama cikin harkokin ta ” wanda hakan yasa ta kafa ma’aikatar cigaban matasa da wasanni”.

A yayin taron an karrama kungiyoyin matasa da suka yi fice, inda karamar hukumar Gabasawa tazo ta daya.

Tun farko ana shi jawabin, Kwamishinan cigaban matasa da harkokin wasanni, Kabiru Ado Lakwaya, ya jinjinawa kokarin gwamnan bisa samar da aikin yi ga matasa.

Majalisar dinkin duniya ce dai ta ware duk ranar 12 ga watan Agusta a matsayin ranar matasa ta duniya don janyo hankalin duniya kan shigar da matasa a dama da su cikin al’amuran cigaban al’umma.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here