Yan Bindiga Sun Kashe Wani Dan Majalisa a Jihar Bauchi

0
159

Yan bindiga sun kashe dan majalisar jiha mai wakiltar kananan hukumomin Baraza/Dass, Ahaji Musa Mante.

Wata majiya ta da ta nemi a boye sunan ta ta bayyanawa kamfanin dillacin labarai na Kasa(NAN) cewa an kashe dan majalisar ne a jiya Alhamis a gidan sa dake Dass.

Majiyar tace yan bindigar da ake zargin yan fashi da makami ne sun kutsa gidan mamacin a tsakiyar dare tare bude masa wuta.

Mai magana da yawun yan sanda a jihar ta Bauchi DSP Ahmad Wakili ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa yan bindigar sun sace mata da ya’yan mamacin.

“Ana cigaba da bincike da zarar an kammala za’a sanarwa da manema labarai” inji mai magana da yawun rundunar yan sandan.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here