Rashin Albashi Mai kyau ne yasa na Fara siyar da Gireba –malamin firamari.

0
253

 

Malam salisu Garba Sheka ,malamin firamare a unguwar Sheka dake karamar hukumar Kumbotso dake jahar Kano,yace rashin albashi Mai kyau ne yasa ya Fara siyar da gireba,duk da cewa Yana da shaidar karatun horar da malamai ta kasa,(NCE)inda yafara koyar da dalibai a makaratun firamari tun a shekara ta 2004.

Rashin kula da Gwannatin take yi ga malamai yasa mun shiga yanani da bama iya ciyarda iyalan mu, mussaman Ni da nake da ya’ya 7,shine Naga dacewar na fara siyar da gireba,duk da cewa na fuskanci kalubale da na Fara siyar da shi idan ake nuna Ni ana dariya,har wasu na rike cikin su tsabar dariya sun ga na kaskantar da kai na Ina tallah,Wanda yanzu haka samu riba dubu 2 ko 3 a Rana.

Na Kan dauki na dubu 8 daga karfe 7 na safe zuwa 12 Rana na siyar,daga baya Kuma na dau na dubu 8 har zuwa dare.

Malam salisu sheka yace sana’ar siyar da gireba tafi Masa albashin da Gwannatin take Bashi a matsayi malamin firamare rufin Asiri.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here