Mahaifi Ya Kulle Dansa Tsawon Shekara 7 A Garejin Gidansa

0
173

Daga Mustapha Adamu

Yan’ sanda sun kubutar da Ahamad Lawan mai shekaru 32 wanda mahaifin sa da kishiyar mahaifiyar sa suka kulle shi tsawon shekaru 7 a daki.

Aliyu wanda yake mazaunin unguwar Farawa Babban Layi dake Mariri, karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano, Yan’sanda da kungiyoyin kare hakkin dan adam sun kubutar dashi ne a yammacin jiya Alhamis.

An daure shi ne a cikin gida bayan iyayen sa sun zarge shi da ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Sai dai wasu mazauna yankin sun ankarar da jami’an tsaro da kungiyoyin kare hakkin dan’adam halin da Aliyu ke ciki.

Bidiyon mutumin ya karade shafukan sadarwa a safiyar yau juma’a inda yake nuna yadda jami’an tsaro suka kubutar dashi daga kejin da aka kulle shi shekaru 7.

Jami’an tsaro sun gayyaco iyayrn mutumin don amsa tambayoyi.

Makota da mazauna yankin sun kadu da jin labarin kulle mutumin.

Mai magana da yawun rundundunar yan sanda reshen jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna tabbatar da faruwar lamarin.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau juma’a , Kiyawa yace rundunar ta samu bayanai a ranar Alhamis da karfe 11:30 na safe cewa Aminu Farawa ya kulle dan sa, Ahmad Aminu a garajin motar sa dake gidan sa tsawon shekara 7 ba tare da bashi cikakken abinci ba da kula da lafiya.

“Tawagar Jami’an atisayen Puff-Adder sun kai daukin gaggawa. Sun kubutar da mutumin tare da kaishi asibitin Murtala inda aka kwantar dashi.

“An kama mahaifin nasa. Binciken farko ya nuna cewa mahaifin ya tabbatar da kulle dan sa shekaru uku bisa zargin shan miyagun kwayoyi, kwamishinan yan sanda na jihar Kano CP Habu A. Sani ya bada umarnin kai lamarin sashin binciken laifuka na hukumar. Inji sanarwar.

A

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here