COVID-19: Gwamnatin Tarayya Tayi Bayanin Ranar Da Za’a Sake Bude Makarantu

0
189

Gwamnatin tarayya tayi karin haske kan ranar da za’a sake bude makarantu domin cigaba da karatu.

Karamin ministan ilimi Chukuemeka Nwajiuba ne yayi karin hasken yayin jawabi na kullum da kwamitin fadar shugaban kasa kan yaki da cutar COVID-19 keyi a Abuja. Inda ya kara da cewa da zarar kwamitin ya kammala hada bayani zai sanar da yan Najeriya lokacin da za a sake bude makarantun.

Sannan ministan yayi nuni da cewa har yanzu kungiyar malaman jami’i’o ta ASUU tana yajin aiki wanda suka fara shi tun watan Maris.

Shima anasa jawabin shugaban kwamitin kar ta kwanan kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha yayi gargadin cewa kowa zai iya kamuwa da cutar.

Sannan ya bayyana cewa dole ne kowa ya kare kansa daga kamuwa daga cutar sannan kada mutane su yi tsammanin cewa cutar baza ta kama yan’uwa da abokan su ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here