Sarakunan Qabilar Igbo Sun Yabawa Buhari Bisa Ayyukan Cigaba da Yake yi a Yankin Su

0
147

Masu rike da sarautun gargajiya a jihar Anambra a yau Talata sun bayyana farin cikin su ga shugaban Kasa Muhammadu Buhari bisa kokarin sa wajen kawo ayyukan cigaban kasa musamman a yankin Kudu maso gabas.

Prince Arthur Eze, ne ya jagoranci masu rike da masarautun gargajiyar zuwa fadar shugaban kasa inda suka samu tarbar shugaban ma’aikata na fadar, Farfesa Ibrahim Gambari, inda ya gode musu tare da fadin cewa ziyarar zata kara karfin gwiwa ga shugab Buhari wajen kara yin ayyukan cigaba a yankin da ma kasa baki daya.

“Kamar yadda ake fadi a sassa daban-daban na kasarna, yayin da ka godewa wani mutum bisa aikin da yayi ma, kana kara masa kwarin gwiwa ne domin yayi ma abin da yafi haka”. Inji shugaban Ma’aikatan fadar shugaban kasa.

Masarautan sun bayyana irin aikace-aikacen da shugaba Buhari yayi a yankin da suka hada da: Gadar Second Njger Bridge, titin Enugu zuwa Onitsha, da titin Enugu zuwa Port Harcourt da Sauran su.

“Mutanen yankin kudu maso gabas na matukar farin ciki, a maimakon su muna cewa mun gode” cewar Basaraken Yankin.

Sannan sun jinjinawa Shugaban Kasa bisa nada yan kabilar Igbo a manyan mukaman gwamnati.

Sarakunan da suka kai ziyarar sun hada da, HRM Eze Dr. Nkeli Nzekwe, HRM Igwe Chuba Mbakwe, HRM Igwe Chijioke Nwankwo, HRH Igwe Anthony Onwekwelu da HRH Igwe Chukuma Bobo Orji.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here