Ranar Matasa Ta Duniya: Atiku Ya Bukaci Matasan Najeriya Su Yaki Annobar COVID-19

0
156

Daga Muhammad Bashir

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar yace matasa suna da rawar da zasu taka wajen yaki da cutar COVID-19, sannan zasu taimaka wajen hana yaduwar cutar.

Atiku, a wata sanarwa da ya fitar a Abuja jiya Talata, a yayin da ake bikin ranar matasa ta duniya, ya bukaci matasa da su bi matakan kariya da hukumar hana yaduwar cutuka ta kasa (NCDC) ta shimfida.

Ranar matasa dai ta duniya ana yin ta duk ranar 12 ga watan Agusta na kowacce shekara, don jawo hankalin gwamnati wajen kula da matasa.

“A wannan lokaci da ake fama da annobar COVID-19, matasa suna da hakki akan su na hana yaduwar wannan cuta, sannan su taimaka wajen bin ka’idojin da hukumar NCDC ta shimfida kamar wanke hannu, sanya takunkumin rufe hanci da baki, kaucewa cunkoso da bada tazara.

“A matsayin shugabanni na yau, da Gobe, ina son dukkan ku da su fadakar tare da wanzar da zaman lafiya gami da kishin kasa”.

Sannan Atiku ya taya murna ga matasan dake fadin duniya ranar matasa karo na 20.

Sannan ya jinjinawa matasan Najeriya bisa kokarin su wajen mayar da Najeriya kasaitacciyar kasa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here