Mutanen Garin Karaye Na Shan Wahala – Hakimi

0
167

Hakimin garin Karaye; Magaji Gari Engineer Shehu Ahmad ya bayyana rabon kayan tallafi ga mabukata a cikin al’umma a matsayin wata babbar hanyar yaki da annobar COVID-19.

Emgineer Shehu Ahmad ya bayyana hakan a wajen bikin rabon kayan tallafi kashi na uku a karamar hukumar Karaye.

Wata sanarwa da jami’in yada labarai na masarauta Karaye, Malam Haruna Gunduwawa ya aikowa da jaridar PRIME TIME NEWS ta tabbatar da cigaban.

Hakimin wanda ya wakilci Sarkin Karaye Alhaji Dr. Ibrahim Abubakar II a wajen taron yayi nuni da cewa mutanen da suke karbar tallafin suna cikin farin ciki duba da yadda suke shan wahala wajen samun abincin daza su ci na yau da kullum.

Sannan ya godewa yan kasuwa da kungiyoyin wayar da kan al’umma da dukkan wadanda suka taimaka wajen rage radadin da mutane suke fuskanta sakamakon annobar COVID-19.

Haka kuma yayi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni su cigaba da rike wannan tsarin har bayan cutar Corona.

Yayin da take jawabi a wajen taron wanda aka gudanar ana tsaka da ruwan sama, Hajiya Aisha Jaafar tace gwamnati na shirin bayar da irin wannan tallafi ga magidanta dubu dari uku.

Shima anasa jawabin shugaban karamar hukumar Karaye Alhaji Abdulhamid Garba Karaye ya bukaci wadanda suka amfana da tallfin da suyi amfani dashi yadda yakamata kar su siyar da shi.

An raba buhun masara mai girman Kilogram 25 da gero, taliya da man girki ga magidanta 670 a yankin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here