Kotu Ta Yanke Hukuncin Jifa Ga Wani Mutum a Kano bisa Laifin yin Fyade

0
155

Kwanaki uku bayan wata kotun shari’a a Kano ta yanke hukuncin kisa ga wani mutum bayan samun sa da laifin yin batanci ga FIYAYYEN HALITTA S.A.W, wata kotun shari’ar ta kara yanke hukuncin kisa ga wani mai suna Mati Abdu, dan shekara 60 ta hanyar jefewa bayan samun sa da laifin yiwa yarinya karama fyade.

Kotun dai tana zamanta ne a unguwar Kofar Kudu kusa da fadar Sarkin Kano.

Yan’sanda sun kama Mati ne a shekarar 2019 bisa zargin yiwa yarinya yar shekara 12 fyade da rana tsaka a kauyen Farsa dake karamar hukumar Tsanyawa a jihar.

Alkalin Kotun, Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya yanke hukuncin kisa ga mutumin ta hanyar jefewa bayan ya saurari shedu, sannan aka tabbatar mutumin yana da aure.

Mai magana da yawun kotunan jihar Kano, Baba Jibo ya tabbatar da yin hukunci a yammacin yau Laraba.

Inda yace, lauyar gwamnati, Barrister Badariyya ta gabatar da dukkan shedun da ake bukata a gaban kotun.

Idan za’a iya tunawa dai a ranar Litinin ne, Wata kotun shari’a dake zamanta a unguwar Hausawa karkashin jagorancin mai shari’a Khadi Aliyu Kani ta yankewa Yahaya sharif hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kama shi da laifin yin batanci.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here