Kananan Hukumomi 20 a Kano Na Cikin Hadarin Samun Ambaliyar Ruwa

0
201

Alhaji Sanusi Ado, babban jami’in dake kula da tsare-tsare na ofishin hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) na Kano yace kananan hukumomi 20 dake jihar Kano na cikin hadarin ambaliyar ruwa a shekarar 2020.

Babban jami’in ya bayyana hakan a Kano wajen taron masu ruwa da tsaki kan wayar da kai wajen magance ambaliyar ruwa da kuma abinda harshashen damunar bana ka iya haifarwa.

Jami’in yace “Kano tana daga cikin jihohin da ake zaton samun ambaliyar ruwa, kamar yadda rahotan shekara na gargadi akan ambaliyar ruwa ya bayyana.

” Wadandanan kananan hukumomin da ake zaton za’a samu ambaliyar ruwa sun hada da; Tarauni, Garun Malam, Rimin Gado, Gaya, Gezawa, Gwale, Shanono, da Gabasawa.

“Ragowar kananan hukumomin sun hada da; Gwarzo, Ungoggo, Warawa, Dawakin Kudu, Dambatta, Bebeji, Kano, Wudil, Kura, Nassaawa, Kano Municipal da Kumbotso.”

Sannan ya kara da cewa , hakan na barazana ga aikin gona, samar da ruwan sha, lafiya, zirga-zirga da ayyukan cigaba a jihar.

“Idan za’a iya tunawa, a shekarar 2012, ambaliyar ruwa tayi sanadiyar rasuwar mutane da dama da asarar dukiya mai yawa.

“Haka kuma, ofishin hukumar NEMA na Kano, daga shekarar 2018 zuwa 2020 ya tattara iftila’in ambaliyar ruwa 41 tsakanin jihohin Jigawa da Kano.

“Na baya-bayan nan shine ballewar gada a Rimin Gado da Karamar hukumar Tofa wanda ya jawo mutane masu karamin karfi rasa muhallin su.

Kamfanin dillacin labarai na Kasa (NAN) ya rawaito cewa masu ruwa da tsaki a taron sun bada gudunmawa wajen samar da hanyar da za’a magance matsalar ambaliyar ruwa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here