Wani Gwamna a Arewa ne Babban Kwamandan Boko Haram A Najeriya -Dr. Obadiah

0
213
  1. Tsohon mataimakin Gwamnan Babban Banki na kasa(CBN), Dr. Obadiah Mailafiya, yace tubabbun yan kungiyar Boko Haram sun tona asirin cewa daya daga cikin gwamnonin arewacin kasarnan ne ke daukar nauyin kungiyar Boko Haram.

Mailafiya ya fadi hakanne a cikin wani shiri mai suna “Morning Crossfire’ wanda ake gabatarwa a gidan rediyon Nigeria Info Abuja 95.1 FM a ranar Litinin.

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin yace ya tattauna da tubabbun yan kungiyar Boko Haram guda biyu da suka tabbatar da masa da gwamnan na Arewa.

Yace, Yan Bindiga da Yan Boko haram duk abu daya ne.

Mailafiya, wanda yayi takarar shugabancin kasa a jami’iyyar ADC, yace yan ta’adda na zirga–zirga da makamai har a lokacin dokar kulle wace cutar Corona ta haifar.

Inda yace ” Wasu daga cikinmu suna da hanyar samun bayanan sirri. Na hadu da wasu daga cikin yan bindiga; mun hadu da wasu daga cikin kwamandojin su, wasu biyu daga ciki mun zauna tare da su ba sau daya ba ba sau biyu ba”.

“Sun fada mana cewa wani Gwamna a Arewacin Najeriya shine jagoran Boko Haram a kasarnan.

” Sun safarar makamai, kudade tare da rarraba su a fadin kasarnan”.

“Nan da shekarar 2022 , suke san fara yakin basasa a Najeriya. Kar kuyi wasa da abin da nake fada, ina da digirin-gir-gir daga jami’ar Oxford, ni ma’aikacin banki ne don haka bama son shashanci.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here