Matasa Miliyan Biyar ne Suka Nemi Shiga Shirin Npower

0
148

Ma’aikatar jin kai da walwalar jama’a tace akalla mutane miliyan 5 ne suke nemi shiga cikin shirin samawa matasa aikin yi na NPOWER.

Ministan jin kai da walwalar jama’a, Hajiya Sadiya Umar Faruq ce ta bayyana hakan ta hannun mai taimaka mata ta hanyar sadarwa, Mrs Halima Oyelade.

“A yayin da aka kawo karshen yin rijistar shirin , matasan Najeriya 5, 042, 0001 ne suka nemi shiga cikin shirin”.

Sannan tace yin rijistar shiga cikin shirin, wacce aka fara a ranar 26 ga watan Yuni, an tsara za’a kammala a ranar 26 ga watan Yuli sai dai an kara wa’adin mako 2.

” Ma’aikatar zata tabbatar da cewa wadanda suka nemi shiga cikin shirin da sauran al’umma sun samu bayanan da ake bukata anan gaba.” Inji ta .

Sannan ministan tace za’a duba masu bukata ta musamman daga cikin wadanda suka nemi shiga cikin shirin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here