Kasar Amurka Ta Cika Alkawarin da Tayiwa Najeriya

0
199

Daga Salisu Hamisu Ali

Kasar Amurka ta mika na’urar taimakawa numfashi guda 200 ga Gwamnatin Tarayya a yau Talata.

Wannan shine cika alkawarin da shugaban kasar Amurka ya dauka yayin tattaunawar su da shugaba Buhari ta wayar tarho a watan Afrilu da ya gabata.

Ministan lafiya, Dr. Osagie Ehanire ne ya karbi kayayyakin daza su taimaka wajen yaki da cutar COVID-19 daga Jakadan kasar Amurka, Mary Leonard a wani taro da aka yi a Abuja.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here